Wednesday, October 10, 2007

muahdu mu lalubo kan zaren

dasunan allah me rahmame jin kai
tsira da aminci su kara tabbata ga manzon tsira da rahma, annabinmu muhammad da duk wadanda suka biyo bayansa
naji dadi da allah ya bani damar bude wannan shafi na musamman wanda nake sadaukar dashi domin tattauna matsalolin dake damun al'ummar mu ciki da waje
inaso nayi amfani da wannan shafi domin tattaunawa da mutane daban daban kowani mutun kan abinda ya kware akansa
kasarmu tana fuskantar barazana dayawa, abubuwa dayawa sun faru wadanda suka hargitsa tsatin zaman takewar mutane ,wasu kuma sun firgita wasu mutanen, a filin siyasa ,addini, al;adunmu,wasanninmu,tsarin karatunmu,yanayin gudanar da jagoranci a kasarmu
da kuma abubuwan dake faruwa da duniya da yanda yakamata mu dauki darasi na kwarai daga garesu ,ance:{idan kaga gemun wani ya kama da wuta seka zubawa naka ruwa}
daga cikin abubuwan da suka jawo hankalina akawai:
1;lalacewar tsarin koyarwa a kasarmu ,wanda shine ya bude kofar duk sauran musibun da muke ganinsu a gabanmu